Shugaba Buhari Ya Tsawaita Zamansa A Birnin Landan Da Mako Guda Domin A Duba Hakoransa.

0 157

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tsawaita zamansa a birnin Landan na kasar Birtaniya da mako guda domin a duba hakoransa.

Tun da farko dai shugaban kasar ya tafi Burtaniya ne a makon da ya gabata domin halartar bikin nadin sarautar Sarki Charles na uku.

A makon nan ne aka shirya zai dawo Najeriya amma yanzu zai tsaya bisa umarnin likitan hakori wanda tuni ya fara zuwa wurinsa.

Mai magana da yawun shugaban kasa Femi Adesina a wata sanarwa da ya fitar jiya da daddare ya ce likitan hakorin na bukatar ganin shugaban kasar nan da wasu kwanaki biyar domin cigaba da duba lafiyar shugaban kasar da tuni aka fara. Tsawaita zaman da shugaban kasar ya yi a birnin Landan ya janyo suka daga wasu ‘yan Najeriya, inda suka ce ya kamata ya ba da fifiko kan matsalolin cikin gida da kuma magance matsalolin tsaron da kasar ke fuskanta.

Leave a Reply

%d bloggers like this: