Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya roki al’ummar jihar Filato su rungumi zaman lafiya, tare da jaddada cewa gwamnatin na yin duk mai yiwuwa domin kawar da duk wani tashin hankali ko fitina.
Shugaban ya yi kiran ne a wata sanarwa dauke da sa hannun kakakinsa, Malam Garba Shehu.
Sanarwar ta ce duk da irin kokarin da gwamnati take yi wajen tabbatuwar zaman lafiya dole sai malaman addinai da sarakuna da sauran shugabannin sun guji amfani da duk wani salo ko yada batutuwan da ka iya ingiza rikici.
Shugaba Buhari ya ce akwai tarin matsalolin da kasar ke fama a yanzu kuma yana da muhimmanci ‘yan Najeriya da sauran kasashe su ke fahimtar irin kokarin da suke yi wajen kawar da duk wasu rigingimu a fadin kasarnan.
A cewarsa, ana kara jami’an tsaro a kauyuka da garuruwan dake fama da rikici a jihar Filato, domin tsare rayuka da dukiyar jama’a a jihar.