Shugaba Buhari ya nada wasu shugabannin hukumomin da suke karkashin Ma’aikatar Ilimi

0 172

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ya amince da nadin sabbin wasu nade-naden shugabannin hukumomin da suke karkashin Ma’aikatar Ilimi.

Daraktan Yada Labarai da Hulda da Jama’a na Ma’aikatar Ilimi Mista Bem Goong, shine ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai a jiya Laraba.

Daraktan Yada Labaran, ya ce sabbin nade-naden sun kunshi Farfesa Akpama Ibar a matsayin Sakataren Zartarwa na hukumar Yaki da Jahilci ta Kasa, da Farfesa Chinwe Anunobi a matsayin Daraktan Janar na hukumar Lura da Dakunan Karatu da kuma Farfesa Musa Maitafsir, a matsayin Shugaban Cibiyar Horas da Malaman Makaranta.

Sanarwar ta ce Shugaba Buhari ya amince da sake nada Farfesa Josiah Ajiboye, a matsayin Shugaban Hukumar Shiryawa Malaman Makaranta Jarabawa, inda zai sake shafe shekaru 5 a matsayin shugaban hukumar.

Kazalika, Shugaba Buhari ya amince da sake nadin Farfesa Bashir Usman, a matsayin shugaban hukumar Lura da Ilimin Makiyaya ta Kasa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: