Shugaba Buhari Ya Kaddamar Da Rukunin Gidajen Zuba Na Naira Biliyan 9 Da Rabi

0 196

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a yau ya kaddamar da rukunin gidajen tarayya dake Zuba a babban birnin tarayya Abuja.
Rukunin gidajen wanda aka gina akan fili mai fadin kadada 18.5, ya kunshi gidaje 748.
Hukumar gidajen tarayya ce ta gina rukunin gidajen.
Da yake jawabi yayin bikin kaddamarwar, shugaban kasar yace rukunin gidajen bangare ne na kokarin gwamnatin tarayya na dakile talauci da samar da gidaje ga jama’a.
Shugaba Buhari yace aikin gina gidajen wanda ya samar da ayyuka da dama, wani bangare ne na alkawarinsa na inganta rayuwar ‘yan kasa.
Da yake amincewa cewa akwai bukatar gwamnati ta kara hobbasa domin karin ‘yan Najeriya su mallaki gidaje, yace gwamnati baza ta yi kasa a gwiwa ba wajen kammala dukkan ayyukan gina gidaje kafin ya sauka daga mulki.
A nasa bangaren, ministan ayyuka da gidaje, Babatunde Raji Fashola, yace an amince da kudin gina gidaje a shekarar 2018.

Leave a Reply