Shugaba Buhari ya bayya yadda zai yi amfani da lokacin da ya rage masa a mulki

0 219

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya tabbatarwa da yan Najeriya da kasashen duniya cewa gwamnatinsa za tayi amfani da sauran shekarun da suka rage mata wajen inganta samun ilimi mai nagarta da kiwon lafiya da kuma habaka kasuwanci.

Shugaban kasar, wanda ya karbi takardun kama aiki daga jakadun kasashe takwas a fadar shugaban kasa, yace ana kokarin tabbatar da matsayin Najeriya na kasar da ake san zuwa domin zuba a jari, da ribar da ake samu a kowane bangare, musamman yawan masu sayayya da tsarin biyan haraji mai sauki, wanda masu zuba jari daga kasashe daban-daban za su ci gajiya.

Jakadun kasashen da suka mika takardun kama aikinsu sune na kasashen Algeria da Vietnam da Tanzaniya da Ivory Coast da Chadi da Somaliya da Jamhuriyar Larabawa ta Sahrawi da kuma Iran.

Shugaban kasar ya gayawa jakadun abubuwan da Najeriya tafi mayar da hankali akai, da kuma bukatar tabbatar da kudirorin da mutane zasu amfana.

Leave a Reply

%d bloggers like this: