Shugaba Buhari ya amince da sauyawa Ma’aikatar Kimiyya da Fasaha suna zuwa Ma’aikatar Kimiyya, Fasaha, da Kasuwancin Zamani
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya amince da sauyawa Ma’aikatar Kimiyya ta Fasaha Suna, zuwa Ma’aikatar Kimiyya, Fasaha, da Kasuwancin Zamani, da nufin sake karfafa bincike da kuma cigaban Masana’antu da harkokin yau da kullum.
Ministan Ma’aikatar Dr Ogbonnaya Onu, shine ya bayyana hakan a taron manema labarai a Abuja, inda ya ce Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya umarci ma’aikatar da dinga sanya idanu kan kudurin gwamnatin tarayya na bunkasa kasuwancin zamani.
Ministan ya ce amincewa da sauya sunan ma’aikatar zai bata damar kirkirar shirye-shiryen da zasu tallafawa fannin kasuwancin zamani, tare da bunkasa ayyukan ma’aikatar.
Kazalika ya ce akwai bam-bam ci a tsakanin sunan Ma’aikatar da kuma sabbin ayyukan da ma’aikatar ta kuduri aniyar aiwatarwa tun bayan sauya mata suna, wanda zata samu damar gudanarwa.