Shugaba Buhari da gwamnonin yankin Arewa 19 ba abin dogaro bane wajen samar da tsaron a cewar Ƙungiyoyin farar hula na Arewa
Kungiyoyin farar hula na Arewa, a karkashin inuwar gamayyar kungiyoyin Arewa, sun bayyana cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari da gwamnonin Arewa 19 ba abin dogaro bane wajen samar da tsaron rayuka da dukiyoyi da yankin ke bukata.
Da yake jawabi ga manema labarai a Minna babban birnin jihar Niger, shugaban kungiyar na yankin Arewa ta tsakiya, Mohammed A. Mohammed, ya ce Gwamnatin shugaban kasa Buhari da gwamnatocin jihohi sun gaza a manyan bangarorin samar da tsaron rayuka da dukiyoyin ‘yan kasa da kuma tabbatar da ingantaccen yanayin tattalin arziki a kasa.
Kungiyar ta jaddada bukatar cewa yazama dole fararen hula su tashi tsaye don tinkarar sabbin hare-haren da ake kaiwa al’umma da kuma arzikin tattalin arzikin kasar.
Mohammed ya bayar da hujjar cewa ya zama dole a dorawa shugaban kasa da gwamnonin jahohi alhakin yawaitar barazana ga rayuwar ‘yan kasa ba tare da wani yunkuri na dakile matsalar ba.
Kungiyar ta kuma yi watsi da shirin da gwamnatin tarayya ta yi na kara farashin man fetur zuwa Naira 340 a shekarar 2022 mai kamawa, inda ta nuna cewa hakan zai kara dagula wahalhalun da rashin tsaro ke haifarwa.