Shirin samar da abinci na Majalisar Dinkin Duniya na shirin bayar da jari da kayan abinci ga gidaje sama da dubu 40 a jihar Yobe

0 142

Shirin samar da abinci na Majalisar Dinkin Duniya na shirin samar da jari da kayan abinci ga gidaje sama da dubu 40 a jihar Yobe a shekara mai zuwa.

Shugabar shirin na samar da abinci a jihar Yobe, Anitha Narahari, ta bayyana hakan a wajen kaddamar da tallafin rayuwa na bana ga ‘yan gudun hijira a jihar.

Narahari ta ce galibin kayayyakin abinci ana kai su ne zuwa lunguna da sakuna na jihar inda mafiya rauni suke zaune.

Ta ce shirin samar da abinci na majalisar dinkin duniya ba zai dakatar da samar da abinci ga marasa galihu ba amma zai cigaba da aikinsa kasancewar tuni shirin ya tsara cigaba da samar da samar da abinci a shekara mai zuwa.

A nasa jawabin, shugaban ofishin shirin samar da abinci na majalisar dinkin duniya a Damaturu, Agbessi Amewoa, ya ce ana gudanar da shirin ne bisa la’akari da kudade da kuma gudunmawar da kasashe da hukumomi masu hannu da shuni ke bayarwa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: