Kimanin Naira miliyan dubu daya ne yan siyasun kasarnan suka tara a matsayin gudun mawa domin ginin jami’ar musulunci ta farko wato Assalam, a karamar hukumar Hadejian jiharnan.
Yan siyasun da suka hadar da gwamnoni da yan majalisu, sun sanar da gudun mawar tasu ne a jiya lahadi, yayin bikin dasa harsashin ginin jami’ar a aka gudanar.
Gwamna Muhammadu Badaru Abubakar, shine ya sanar da gudun mawar naira miliya 250, da gwamnonin Kano, Sokoto, Kebbi, Katsina da kuma shi kansa suka bayar.

An ruwaito cewa wani mutum da ya nemi a sakaye sunansa, ya bayar da gudun mawar naira miliyan 500, yayinda jagoran jam’iyyar APC na kasa Bola Ahmed Tinubu, ya bayar da miliyan 10, sannan yan majalisu da suka tara naira miliyan 150.
Shirin samar da jami’ar irinta ta farko a Najeriya na zuwa ne karkashin kungiyar Jama’atu Izalatul Bid’a Wa Iqaamatu Ssunah, wadda shugabanta Sheik Abdullahi Bala Lau ke jagoranta.
- Majalisar Dokokin Legas ta sake zaɓen Obasa a matsayin kakakinta
- An yi garkuwa da wani ɗansanda a Abuja
- Gwamnatin Jihar Yobe ta bayar da tallafin karatu da ya kai Naira biliyan 2.22 ga dalibai 890
- Kungiyar NANS ta yi barazanar fara zanga-zanga a fadin Najeriya
- Kotun ta yi watsi da bukatar hana jami’an gwamnati tafiya kasashen waje don neman magani
Bala Lau yace manufar hakan itace samar da wata dam aga matasa domin rabauta da iliman boko da Addina a wuri guda.
Ya kuma ce jami’ar ba wai tayi iyaka ne ga al’umar musulmai kadai ba, ill aga duk wanda ya cike sharudan da ta gindaya domi samun gurbin karatu.