Kwamitin karta kwana kan cutar COVID-19 wanda fadar shugaban kasa ta kafa, ya bayyana labaran da ke yawo cewa, daya daga cikin likitocin kasar Chaina wanda suka zo Najeriya yana dauke da cutar COVID-19 a matsayin labaran kanzon kurege.
Ministan labarai da al’adu, Alhaji Lai Muhammad, wanda daya ne daga cikin membobin kwamitin ya karyata labarin da ake yadawar.
Ministan wanda ya bayyana cewa kwamitin yanayin duk wata mai yiwa wajan yaki da cutar COVID-19, bisa goyon bayan gwamnati a kokarin dakile yaduwar annobar da ke cigaba da mamaya.
Ministan wanda a kwanakin baya ya dauki lokaci yana shawartar mutane kan kiyaye yada labaran kanzon kurege, haka kuma ya shawarci yan Najeriya da masu marawa gwamnati baya wajan daina yada bayanan da basu fito daga hukumomin da ke da alhakin fitar da su ba, ko kuma wanda ba hukumar dakile yaduwar cututtuka bace ta fitar.