Shekau ya fashe da kuka yana neman Taimako

0 229

A cikin wani sabon sakon murya Audio, shugaban kungiyar yan ta’adda ta Boko Haram Abubakar Sheko ya fashe da kuka yana neman agaji daga irin ragargazar da sojojin Najeriya ke yi masa.

Sakon Muryar mai tsawon 1:22 ya kunshi Muryar sa a inda yake neman taimakon Allah ya tsare daga lugudan wutar da suke sha.

A baya-bayan nan dai sojojin Najeriya sun matsa kaimi kan kawo karshen yan ta’addan a maboyarsu.

Daily Nigeria ta rawaito cewa shekau yayi magana ne cikin harshen kanuri yana bayyana irin yadda sojojin suka takurawa rayuwarsu a cikin watan azumi

Shekau Dai ya saba yin bidiyo ko sakon murya yana dariya da yin suka da habaici amma sai ga shi yanzu yana neman taimako.

Kwanan baya an ta yada labarun cewa yana neman sulhu don mika wuya ga sojojin Najeriya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: