Gwamnan jihar Jigawa Alhaji Muhammadu Badaru Abubakar ya ce nan da shekrau 15 masu zuwa man fetur zai rasa darajarsa a fadin duniya.
Gwamna Muhammad Badaru Abubakar ya furta hakan ne yayin wani taro kan harkokin noma a Damaturu babban birnin jihar Yobe,Ya ce dole ne ƙasar nan ta dena dogaro ga man fetur a matsayin babban abinda ke samar mata kudin shiga, idan har tana son ta cigaba da zama da kafar ta.
Gwamnan na Jigawa ya yi hasashen cewa nan da shekaru 15 dake tafe man fetur ba zai yi daraja ba a kasuwani duba da irin cigaba na fasaha da ake samu a kasashen duniya.
Muhammad Badaru Abubakar, ya bayyana damuwa akan irin albarkatun da Allah ya bawa ƙasar nan, amma ta dogara da man fetur lokaci mai tsawo wadda hakan ya haifar da matsaloli ga sauran bangarorin tattalin arziki.
Sannan ya shawarci jihar Yobe ta mayar da hankali akan noman Ridi da Karo wadda a cewarsa jihar ce ke noma mafi kyawu da ake nema a kasuwanni.