Sheik Yahya Jingir ya yi kira ga ƴan Najeriya da su koma kare kawunansu daga hare-haren ƴan bindiga

0 416

Shugaban kungiyar Jama’atu Izalatil Bidia Wa-Ikamatis Sunnah (JIBWIS) na kasa, Asheikh Muhammad Sani Yahya Jingir, ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su koma kare kawunansu daga hare-haren da ake kaiwa garuruwansu.

Malamin ya yi wannan kiran ne a wata hira da ya yi da ‘yan jarida a Dutse, inda gargadin cewa lokaci ya yi da ‘yan Nijeriya za su bijirewa duk wata barazana da fargabar masu kawo hari garuruwansu.

Ya kuma yi kira ga gwamnatin tarayya da ta binciki yadda wadanda ke da alhakin tsare rayuka da dukiyoyin ‘yan Najeriya ke kashe kudaden da ake basu.

Dangane da yajin aikin da kungiyar kwadago ta kasa za ta shiga kan sabon shirin karin kudin man fetur da za a fara daga watan Fabrairu na shekara mai zuwa, ya ce ba ya goyon bayan duk wani yajin aiki ko zanga-zanga a kasarnan, haka ma ba ya goyon bayan shirin kara farashin man fetur daga gwamnatin tarayya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: