Sharaɗin Salman Khan kafin fitowa a kowanne Fim

0 400

Jarumi Salman Khan babban mai taka rawa ne a masana’antar shirya fina-finai ta Bollywood wanda tauraruwarsa ke haskawa har yanzu duk da girma da tarin shekarunsa.

Sai dai wani abu da ba kowa ya sani ba game da Jarumin shi ne, ba yana da wata tsattsauran dokar da dole sai an amince kafin ya yarda ya fito a cikin Fim.

Wannan doka kuwa ita ce; ba zai yarda a cikin kowanne irin Fim yayi Sumbatar laɓɓa ba (Kiss) ko kuma zurzurfar sosayyya (Romance).

A cewarsa yana jin kunyar yadda jama’a zasu kalle shi musamman ma yan gidansu tunda har mahaifiyarsa tana kallo.

Don haka duk mai son ya fito a cikin Fim dinsa dole ne ya amince da wannan doka ko kuma ya nemi wani jarumin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: