Jami’an hukumar kashe gobara da na NEMA sun samu nasara kashe wata gobara da ta tashi a kasuwar Fallujah Shopping Mall da ke birnin Yola ta jihar Adamawa.
Cikin wata sanarwa da hukumar bayar da agajin gaggawa ta NEMA ta wallafa a shafinta na X, ta ce gobarar – wadda ta tashi cikin daren da ya gabata – ta janyo asarar dukiyoyi na miliyoyin kuɗi.
NEMA ta ce jami’anta da na kashe gobara da na jami’an hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Adamawa, sun samu nasarar kai ɗauki domin kashe wutar.
”Babu labarin rasa rai, amma shaguna 12 sun ƙone ƙurmus, galibi na sayar da kayan wayoyin hannu, lamarin da ya haifar da asarar dukiya mai tarin yawa”, a cewar sanarwar.
Kawo yanzu hukumomi sun ce suna ci gaba da bincike domin gano musabbanin gobarar.
Gobara a kasuwannin Najeriya, wani abu ne da ya jima yana haifar da ɗimbin asarar dukiyoyi, inda a lokuta da dama hukumomi ke cewa za su gudanar da bincike domin ɗaukar matakai.