Senator Sabo Nakudu ya bada gudummawar kwamfutoci ga dalibai biyar-biyar na kananan hukumomin 7

0 267

Dan majalisar Dattawa mai wakiltar Jigawa ta tsakiya, Senator Sabo Muhammad Nakudu, ya bada gudummawar kwamfutoci ga dalibai 35 ga dalibai biyar-biyar na kananan hukumomin 7 da yake wakilta wadanda suke karatu a manyan makarantu daban-daban.

Da yake mika kwamfutocin ga daliban a ofishin Kungiyar ci gaban masarautar Dutse, Senator Sabo Nakudu ya ce ya bada kwamfutocin ne da nufin taimakawa daliban wajen harkokin karatunsu bisa la’akari da yadda fasahar tattara bayanai da sadarwa ke da tasirin a wannan zamani.

Sanatan wanda ya samu wakilcin mai taimakawa gwamna kan harkokin kananan hukumomi Alhaji Khalid Ibrahim, ya bukaci daliban su yi amfani da kwamfutocin kamar yadda yakamata domin samun nasarar a harkokin karatunsu.

A jawabinsa na maraba, shugaban kungiyar cigaban masarautar Dutse, Khadi Isa Jibrin Gantsa, ya ce kungiyar tana kokarin fadakarwa da kuma jawo hankalin al’ummomin masauratar domin suyi aiki tare wajen kawo cigaba mai dorewa ba tare da la’akari da siyasa ko yanki ba inda ya bukaci mawadata su bada gudummawa sosai wajen bunkasa harkokin ilimi.

A nasa jawabin, Sakataren kungiyar Dakta Ado Garba Jangargari, ya yabawa Senator Sabo Muhammad Nakudu bisa mu’amala da kungiyar wajen samar da ababen more rayuwa ga jama’a inda ya bukaci fitattu daga cikin al’ummomin masarautar Dutse da ke cikin gwamnati ko kasuwanci da su hada kai da kungiyar wajen aiwatar manofifin cigaba.

Da suke jawabi a madadin daliban da suka amfana, Abdul’Aziz Umar Jahun na jami’ar tarayya dake Dutse da kuma

Ummukhulthum Umar Abbas da ke jami’ar Sule Lamido Kafin Hausa, sun godewa Sanatan bisa wannan gudummawa inda suka roki fitattu a cikin al’umma da ‘yan kasuwa da su tallafawa harkokin ilimi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: