SEMA ta raba tallafi ga manoman da ambaliyar ruwa ya shafa a Jigawa.

0 224

Hukumar Agajin Gaggawa ta jihar Jigawa (SEMA) ta raba kayayyakin tallafi ga manoman da ambaliyar ruwa ya shafa shekaru biyu da suka gabata a karamar hukumar Buji.

Daraktan gudanarwa na hukumar Alhaji Sabo Ibrahim ya bayyana hakan a lokacin rabon kayayyakin.

Yace sakamakon rahotan da hukumar ta karba daga karamar hukumar ya sanya gwamna Badaru Abubakar ya bada umarnin baiwa kananan hukumomin ragowar kayayyakin agajin da aka bayar a shekarar 2018 domin rabawa manoman da ambaliyar ruwan ta shafa.

A jawabinsa mataimakin shugaban karamar Buji, Ahmed Zubairu Gantsa, ya ce gwamnatin tarayya ta bullo da managartan tsare tsare domin tallafawa rayuwar alummar kasarnan. Ya kuma jinjinawa gwamnatin jihar Jigawa bisa kula da rayuwar wadanda ambaliyar ta shafa inda ya bukaci manoman dasu yi cikakken amfani dashi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: