Sauran Kiris Duk Masu Korona A Jigawa Su Warke

0 205

Gwamnatin jihar Jigawa ta sanar da cewa marasa lafiya 222 daga cikin 283 da suke fama da cutar corona a jihar an sallame su.

Gwamna Muhammadu Badaru Abubakar ya sanar da hakan jiya Litinin lokacin da yake jawabi ga manema labarai a Dutse.

Yace an sallami marasa lafiyar saboda sun warke daga cutar corona.

Gwamnan ya kuma sanar da cewa gwamnatinsa ta dage dokar kulle data hana cin kasuwa a jihar.

A cewarsa, Almajirai 120 na daga cikin wadanda aka sallama, wanda ya kawo saura Almajirai 2 kacal da basu gama warkewa ba, suka rage a wajen killace mutane.

Leave a Reply

%d bloggers like this: