Sashin Shari’a ya samu tallafi na musamman a Jigawa

0 198

Kwamishinan sharia na jihar Jigawa Dr Musa Adamu Aliyu yace an rabawa lawyoyin dake aiki a maaikatar sharia kananan komputa domin inganta aiyukansu.

Ya sanar da hakan ne jim kadan da rabon komputocin ga lawyoyin, inda ya ce komputocin zasu taimakawa lawyoyin wajen samun saukin yanke hukunci.

Kwamishinan ya bayyana cewar lawyoyin sun nuna matukar jin dadinsu ga gwamna Muhammad Badaru Abubakar da babban daraktan hukumar fasahar sadarwa ta kasa Kashifu Abdullahi bisa samar da komputocin ga maaikatar sharia ta jiha.

Inda yace mafarkinsa na ganin kowane lawya a maaikatar sharia ya samu komfuta ya cika a lokacin mulkinsa.

A nasa jawabinsa shugaban kungiyar jamian lawyoyi ta kasa reshen Jigawa Barista Mustapha Bello Adamu ya yaba da kokarin lawyoyi da kuma bada tabbacin yin cikakken amfani da komfutocin wajen inganta aiyukansu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: