Mai alfarma Sarkin Musulmi Sultan Muhammad Sa’ad Abubakar na III, yayi kira ga hadin kai daga shugabannin addinai domin dakatar da cusa kiyayya da furta kalaman kiyayya.
Shugaban majalisar koli na harkokin addinin musulunci ya ce wasu ƴan barandan siyasa na barazana ga tarihin Najeriya da na al’ummarta.
A cikin wani saƙon taya murna na bukin Easter da Sarkin Musulmin ya aika wa shugaban Ƙungiyar Kiristocin Najeriya, Daniel Okoh, ya ce lamarin ‘aiki ne na Shaiɗan, wanda makircinsa mai rauni ne.’ Kamar yadda Alƙur’ani ya bayyana.
A cikin jawabin nasa, mai dauke da sa hannun Mataimakin shugaban Majalisar Ƙoli, ta Lura da Harkokin Addinin Musulunci na kasa Farfesa Salisu Shehu, Sarkin ya buƙaci shugaban na CAN ya haɗa hannu da Ƙungiyar ta Musulunci wajen ganin an rage yadda limamai da fastoci ke cusa wa mabiyansu ƙiyayya ta siyasa da kuma munanan kalamai.
Ya bayyana bikin na easter a matsayin wata dama da ake da ita wajen hada kan najeriya, da yada soyayya da kaunar juna, addu’o’i da nuna kyawawan dabi’u da neman gafarar mahalicci.
Daga ƙarshe mai alfarma Sarkin Musulmin ya taya al’ummar Kirista murnar zagayowar ranar Easter tare da addu’ar ci gaban Najeriya.
- Comments
- Facebook Comments