Sarkin Katsina Ya Kaddamar Da Gidauniyar Jin Kai.

0 271

Mai martaba Sarkin Katsina, Dr Abdulmumini Kabir Usman, a jiya ya kaddamar da gidauniyar jin kai mai suna the Emir of Katsina Foundation for Peace.

Haka zalika, za ta tallafa wa gwamnatin jihar wajen  magance matsalolin tada kayar baya.

Da yake karin haske kan makasudin kafa gidauniyar, Sarkin, ta bakin shugaban kwamitin amintattu na gidauniyar  Wazirin Katsina, Sanata Ibrahim Ida, ya ce za ta kuma taimaka wa wadanda rikicin ya shafa tare da tilasta musu barin gidajensu don zama ‘yan gudun hijira.

Ya ce, Gidauniyar za ta kuma taimaka wa marayu da mabukata, da kayan magunguna, da kiwon lafiya da shawarwari.

Ya kara da cewa gidauniyar za ta kuma taimaka wa matasa masu sana’o’i daban-daban ta yadda za su kasance masu dogaro da kai da kuma taimakawa hukumomin da abin ya shafa wajen magance matsalolin shaye-shayen miyagun kwayoyi. Babban abin da ya fi daukar hankali a taron kaddamarwar da aka gudanar a fadar sarkin shi ne rabon kayan agaji da suka hada da tufafi da kayan abinci ga wasu daga cikin wadanda suka amfana.

Leave a Reply

%d bloggers like this: