Mai martaba sarkin Hadejia kuma shugaban majalissar sarakunan jihar nan Alhaji Adamu Abubakar Maje ya bukaci gwamnati da ta gudanar da aikin sanyawa gidaje da unguwanni lambobi domin inganta alamurran tsaro.
Sarkin ya bada shawarar ne a lokacin hawan Bariki na karamar salla da aka gudanar a masarautarsa.
Dr Adamu Abubakar Maje ya kuma ce akwai bukatar yiwa titina sunaye domin kara kyautata alamurran tsaro a garuruwa.
Sarkin ya bukaci gwamnati data kara bullo da tsare tsare na samar da aiyukan yi ga matasa domin rage zaman kashe wando.
A jawabinsa wakilin gwamna kuma sakataren gwamnatin jiha Mallam Bala Ibrahim ya ce gwamnati tana godewa sarakuna bisa irin shawarwarin da suke bata wajen cigaban jihar nan.
Ya ce gwamna Umar Namadi yana aiwatar da manufofi 12 domin ciyar da jihar nan gaba tare da alkawarin gabatar da bukatun sarkin ga gwamna.