Sarkin Daura ya magantu akan bawa ɗan gidan shugaban ƙasa Muhammadu Buhari sarautar gargajiya

0 327

mai martaba sarkin Daura Daura, Alhaji Umar Farouk ya magantu akan bawa dan gidan shugaban kasa Muhammadu buhari, Yusuf sarautar gargajiya.

Yusuf, wanda shine Da namiji tilo, cikin yayan shugaban kasa, ana sa ran cewa a ranar asabar ne, za’a nadashi a matsayin Taban Daura kuma hakimin Kwasarawa.

Yayin dayake zantawa da manema labarai, mai martaba sarkin, jim kadan bayan kammala nada sabbin hakimai 4 a masarautar.

Yace sun dauki wannan matakin ne domin kada sarautar tayi yawo a kasar nan, kuma kada Abuja ko Yola subawa Yusuf wata sarautar, kasancewar Yola ce mahaifar Aisha buhari musamman idan shugaban kasa ya kammala wa’adinsa a 2023.

Hakiman da aka nada a yau, sunhada da Armaya’u Bello, a matsayin Sarkin Gabas na Kwasarawa da kuma hakimin Fatautawa da dai sauransu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: