Sanata Oluremi Tinubu da Nuhu Ribadu za su jagoranci addu’ar neman sauƙi ga Najeriya

0 139

Uwargidan shugaban ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu da mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu za su jagoranci addu’a ta musamman domin neman sauƙin matsalolin da Najeriya ke fuskanta.

Za a gudanar da addu’ar ne ƙarƙashin jagorancin jagororin addinin Musulunci da Kirista, domin neman taimakon Allah a kan ƙalubalen da suka yi ƙasar dabaibayi.

Chief Segun Balogun Afolorunikan, wanda shi ne darakta-janar na shirya addu’ar ta ƙasa ne ya sanar da hakan a Abuja,.

Ya ce akwai buƙatar kowa ya bayar da nasa gudunmuwar domin magance matsalar da ƙasa ke fuskanta, inda ya nanata cewa haɗin kai na da muhimmanci wajen shawo kan dukkan matsala. A cewarsa bayan addu’ar, akwai cewa yaƙinin Allah zai buɗe hanyoyin samun sauƙi, yana mai cewa Najeriya za ta shiga shekarar 2025 cikin walwala.

Leave a Reply

%d bloggers like this: