Sanata Ibrahim Hassan ya kai agaji ga wadanda ambaliya ta shafa

0 229

A nan jihar Jigawa, yayinda al’umma ke cikin halin damuwa sakamakon ifti’la’in ambaliyar ruwa da tayi sanadin muhallai da gonakinsu, a kokarin saukaka radadin zukata, sanatan jihar mai wakiltar santoriyar gabas Barrister Ibrahim Hassan, ya bayar da gudun mawar kayayyakin tallafi ga wadanda abin ya shafa a karamar hukumar Kriskasamma.

Da yake mika kayayyakin a madadin Sanatan, shugaban kungiyar yan kasuwar masarautar Hadejia Alhaji Idris Maji Dadin Jabo, yace kayayyakin sun kunshi fatun buhu 100, buhunan gari 5, buhun sukari 2 da kuma tabarmi 120.

Da yake karbar kayayyakin, shugaban karamar hukumar Alhaji Salisu Garba Kubayo, ya yaba da kokarin sanatan, tare da alkauranta rabon kayan a fadin mazabun karamar hukumar 5.

Saurari hirar da wakilinmu yayi da Sanatan da kuma bubuwa da ya fada

https://t.me/sawabafm/103

Leave a Reply

%d bloggers like this: