Sanata Dalladi Sankara ya gwangwaje ‘yan jam’iyarsa da miliyan 36 dan shan ruwa

0 204

Sanata mai wakiltar Jigawa ta Yamma a majalisar Dattawa, Abdullahi Danladi-Sankara ya baiwa ‘ya ‘yan jam’iyarsa ta APC naira miliyan N36 kudin shan ruwa cikin wannan watan Ramadan mai alfarma.

Sanata Danladi-Sankara yace za’a raba kudaden ne wa ‘yan jam’iyya da wasu mabukata a kananan hukumumi 12 da yake wakilta a majalisar dattawa.

Yayi kira ga yan mazabarsa da al’ummar Jihar Jigawa da suyi amfani da damar wannan wata mai alfarma suyiwa kasa addu’a domin samun zaman lafiya da arziki mai yalwa.

Dama duk shekara a cikin watan Ramadan ina baiwa masoya da ‘yan jam’iya kudin shan ruwa domin na rage masu radadin rayuwa na yau da gobe, inji Danladi-Sankara.

Kudaden za’a rabasu ne a kananan hukumumi da suka hada da Babura ,Garki ,Gagarawa, Gumel, Gwiwa, Kazaure, Maigatari, Ringim, Roni, Sule Tankarkar, Taura da kuma Yankwashi.

Sanatan yace kowacce karamar hukuma ambata kasunta na naira N3 million, yan jam’iyya masu rike da makaman iko zasu raba a junansu naira N1.5 million yayin da sauran ‘yan jam’iyya zasu raba N1.5 million.

Wasu’ yan jam’iyya da suka amfana sun yi wa sanatar addu’o’in samun nasara a rayuwa da fatan cewa Allah ya kaimu shekarar zabe ta 2023.

Shi dai Sanata Danladi-Sankara yana daya daga cikin manya ‘yan siyasar Jihar Jigawa da ake zaton jam’iyar APC take so ya yi mata takarar gwamna saboda karbuwarsa a Jihar.

Amma shi sanatan har yanzu bai fito ya bayyana ra’ayin sa ba dangane da takara a 2023.

Leave a Reply

%d bloggers like this: