Sanadiyyar abinci mai guba mutane 10 sun mutu a arewacin Najeriya

0 240

A kalla mutane 10 ne suka mutu wasu mutanen 400 aka kwantar a asibiti sakamakon ta’ammali da kayan abinci masu guba a jahar Kano, dake arewa maso yammacin Najeriya, wani jami’in yankin ne ya tabbatar da hakan.

Aminu Ibrahim Tsanyawa, kwamishinan lafiya na jahar, ya tabbatar da yawan adadin mutanen da suka mutu yayin da yake karin haske kan faruwar lamarin ga ‘yan jaridu a birnin Kano ranar Alhamis, ya kara da cewa, a halin yanzu kusan mutane 400 ne ke kwance a asibitoci mallakin jahar, yayin da mutane 50 daga cikin adadin ake basu magunguna dake da alaka da ciwon koda.

Tsanyawa ya gargadi al’ummar jahar dasu yi kaffa-kaffa wajen shan abubuwa marasa inganci wadanda ake zargin su ne suka haddasa lamarin a jahar.

Kwamishinan yace, a kwanakin baya ma’aikatar lafiyar jahar ta bada sanarwar cewa an samu barkewar bakuwar cuta wacce aka gano tana da nasaba da shan kayan hada lemuka marasa inganci.

Ya kara da cewa, shan irin wadannan kayayyaki marasa inganci yana haifar da cutar koda, tare da yin illa ga sauran sassan jikin dan adam.

Leave a Reply

%d bloggers like this: