Adadin mahajjata da masu ibadar Umrah da suka ziyarci Masallacin Harami a daren jiya 17 ga watan ramadan ya zarce miliyan 1.
Babban fadar shugaban kasa mai kula da harkokin masallatan Harami biyu ta tanadi motoci dubu 5 na yau da kullum da kuma motocin lantarki kusan dubu 3, masu aiki da mahajar Naql dake bin did-digi.
Bugu da kari, ta dauki ma’aikatan Saudiyya 200 da suka cancanta su sa ido a kan ma’aikata maza da mata dubu 4.
Ma’aikatan sun hada da masu aikin wanke Masallacin Harami sau 10 a kowace rana, tare da shirya kwalaben ruwan Zamzam dubu 7, wadanda ake rabawa maniyyata ta hannun ma’aikata 800.
Haka kuma an raba kwantena dubu 4 da 500 na ruwan zamzam a duk fadin babban masallacin juma’a, wanda ta hanyarsa ake shan kusan lita dubu 500.
- Comments
- Facebook Comments