Sama da mutane Milyan 2 ne suka isa kasar Saudiya domin gudanar da aikin Hajjin bana

0 349

Sama da mutane Milyan 2  daga sassan kasashe na duniya ne suka isa kasar Saudiya domin gudanar da aikin Hajjin bana,inda suka fara hawan Arfa a yau daya daga cikin muhimman rukunan aikin Hajji.

Alhazan sun fara tafiya Mina daga Makka da nufin yin Arfa wanda wannan ne alamar aikin Hajjin ya fara.

Alhazan yanzu haka na Filin Arfa domin yin Sallar Azahar da La’asar, inda zasu yi addu’o’in neman gafara, Rahama,Afuwa da neman Albarka daga Allah Ta’ala, tare da neman samun zaman lafiya ga daukacin Musulmi.

Bayan faduwar rana ne, Alhazan zasu koma Muzdalifa inda zasu kwana a can kafin daga bisani su koma Minna bayan sallar Asuba, inda zasu yi jifan Jamrah.

Asibitoci na aiki karkashin ma’aikatar lafiya ta Saudiya domin kulawa da lafiyar Mahajjatan.

Ma’aikatar lafiya a kasar tace,fiye da gadaje 900 aka samar a asibitoci hudu, mai cike da kayan aiki domin karbar wadanda suka fadi saboda rana da kuma zafi da ma bada kulawar gaggawa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: