Sama da mutane 47 ne suka mutu sakamakon ambaliyar ruwa da zabtarewa kasa

0 215

Mahukunta a Kasar Tanzania sun ce sama da mutane 47 ne suka mutu sakamakon ambaliyar ruwa da zabtarewa kasa.

Lamarin Ya faru ne kusa da tsaunin Hanang inda shugabar kasa Samia Saluhu Hassan ta tura jami’an tsaron kasar domin taimakawa da ayyukan ceto.

Sannan tace akwai gine-gine da gidajen da suka ruguje.

Ambaliyar dai ita ce mafi girman kalubalen yanayi a Tanzaniya, wanda ke shafar dubbannin mutane a kowace shekara.

Gabashin Afirka ya fuskanci mummunar ambaliyar ruwa da zabtarewar kasa a shekarar 2023, wanda wani bangare ya haifar da sabon yanayi na El Niño.

Ko a watan da ya gabata ruwan sama mai karfi ya haddasa mutuwa da kuma rusa kadarori a babban Birnin kasar Dar es Salaam da kuma yankunan Kigoma,Kigera, Geita da Unguja.

Hukumar dake kula da yanayi ta kasar ta yi hasashen cewa za a cigaba da fuskantar ruwan sama mai karfi a wannan watan a kasar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: