Sama da mutane 2,000 ne suka mutu sakamakon girgizar kasa a yammacin Afghanistan

0 215

Adadin wadanda suka mutu a girgizar kasar yammacin Afghanistan ya haura dubu 2 kamar yadda gwamnatin Taliban a kasar ta bayyana, ana ci gaba da gano gawarwakin mutanen a karkashin baraguzan gine-gine.

A cewar hakumomi, sama da gidaje dubu 1,300 ne suka ruguje a girgizar kasar ta ranar asabat mai karfin maki 6.3, biyo bayan girgiza 8 mai karfin gaske, wanda ta mamaye yankin mai nisan kilo mita 30 daga arewa maso gabashin birnin Herat.

A kauyuka, yankin gundumar Zinda, mazauna yankin da dama sun kauracewa gidajensu, yayin da tawagar kai agaji ke cigaba da hako gawarwakin mutane a karkashin baraguzan gine-gine a jiya Lahdi. Kayan agajin da suka isa yankin da ibtila’in ya auku sun hada da Abinci, ruwa, tantuna, barbuguna da  likkafani ga wadanda suka rasu da kuma motocin hako da tebura.

Leave a Reply

%d bloggers like this: