Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya ce sama da mutum miliyan ɗaya ne ambaliyar ruwa ta shafa a Maiduguri.
Gwamnan ya bayyana haka ne yayin da yake raba kayan abinci da kuma sauran abubuwan buƙata ga mutanen da aka tsugunar a sansanin ‘yan gudun hijira na Bakassi da ke cikin Maiduguri.
Gwamna Zulum ya kuma tabbatar da karɓar tallafin naira biliyan uku daga gwamnatin tarayya, wanda za a yi amfani da shi wajen tallafa wa waɗanda lamarin ya shafa.
Ya ce gwamnati za ta kafa wani kwamitin lafiya domin duba daƙile yiwuwar ɓarkewar cutuka a sansanon ‘yan gudun hijirar
Gwmanan ya kuma ce tuni aka fara aikin ceto a yankun da suka fuskanci ambaliyar domin gano waɗanda suka rasa rayukansu.