Akalla mayakan Boko Haram 82 ne aka kashe a wani rikicin cikin gida mai alaka da kabilanci da ya barke tsakanin mayakan.
Lamarin ya faru ne a karamar hukumar Kukawa ta jihar Borno.
Majiyoyin cikin gida da na jami’an tsaro da ke zaune a Baga da kuma yankunan tafkin Chadi sun tabbatar wa manema labarai faruwar lamarin a jiya Laraba.
Daya daga cikin majiyar ta ce rikicin ya barke ne bayan kashe mayakan Boko Haram bakwai da suka fito daga kabilar Buduma.
Ya ce kwamandansu ne ya kashe mayakan a tsibirin Bukkwaram, bayan yunkurin da suka yi na mika wuya ga rundunar sojin Najeriya a ranar Talata da ta gabata.
Ya ce an kira taro, kuma dukkan kwamandojin, ba tare da la’akari da kabilarsu ba, sun cimma matsaya kan cewa mayakan ba su da ‘yancin barin wurin zuwa wuraren da suka zaba.
Wata majiyar tsaro a yankin ta shaida wa ‘yan jarida cewa galibin mayakan da suka rasa rayukansu an san fuskokin mayakan Boko Haram da suka tsere daga garuruwan Baga, Doron Baga da Kukawa zuwa Jamhuriyar Nijar da sauran sassan yankin Sahel.