Sama da kashi 60 na manoma basa amfani da ingantaccen iri a jihar Jigawa

0 176

Gwamnatin jihar Jigawa tace sama da kashi 60 na manoma basa amfani da ingantaccen iri a harkokin su na noma.

Mai bawa gwamna shawara kan harkokin Noma Saifullahi Umar ne ya bayyana haka, a wani taron yini biyu kan shirin noman shinkafa da hukumar bunkasa aikin gona ta jiharnan-JARDA ta shirya.

Yace akwai bukatar gaggauta cike gibin da ake da shi na rashin samun nagartaccen iri da manoma ke fuskanta tsawon shekaru.

Saifullahi yayi bayanin cewa kashi 30 zuwa 35 na amfanin gona ya ta’allaka ne da irin da manomi yayi amfani dashi.

Ya jajanta yadda manoma suka rika tafka asara a sakamakon rashin ingantaccen irin da zasu yi amfani dashi a gonakinsu. Yace shirin na noman shinkafa wanda aka yiwa lakabi da Rice Millionaires ana sa ran zai sauya tunanin matasa daga noman gargajiya zuwa noma dan riba a zamance, bugu da kari shirin zai samar da isashshen ingataccen iri ga manoma domin bunkasa samar da amfanin goma mai yawa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: