Sama da fursunoni 53,000 ne ke jiran shari’a a gidajen yarin Najeriya

0 31

Rahotanni daga Hukumar Gyaran Hali ta Najeriya sun bayyana cewa sama da fursunoni 53,000 ne ke jiran shari’a a gidajen yari.

Adadin da aka sabunta a ranar 24 ga watan Fabrairu na nuna cewa jimillar fursunonin da ke gidajen yari sun kai 80,100, inda 26,846 daga cikinsu aka yanke wa hukunci kawai.

Matsalar jinkirin shari’a na kara dagula halin cunkoso a gidajen yari, abin da ya sa mukaddashin shugaban hukumar, Sylvester Nwakuche, ya kuduri aniyar rage yawan masu jiran shari’ar.

Ministan harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ya ce nan da watan Oktoba za a kaddamar da shirin gyara gidajen yari, domin tabbatar da cewa tsarin yana da inganci da tsari mai kyau.

Leave a Reply