Tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar APC daga Arewa-maso-Yamma, Salihu Muhammed Lukman ya fice daga jam’iyyar.
A sanarwar da ya fitar a ranar Laraba, Lukman ya ce ya fita daga jam’iyyar ne saboda babu adalci a cikin ta.
Ya kuma zargi shugaba Bola Tinubu da ƙin barin a kawo canje-canje a jam’iyyar.
Tun a baya-bayan nan Lukman ya sha caccakar APC a gurare da dama.