Sakon Mai Martaba Sarkin Hadejia Ga Magada Annabawa

0 623

Mai Martaba Sarkin Hadejia, Dr. Alhaji Dr. Adamu Abubakar Maje (CON), yayi kira ga limamai a masarautarsa da su kara himma wajen neman Karin ilimi domin sauke nauyin dake wuyansu yadda ya kamata.

Sarkin yayi wannan kirane lokacin da yake nada sabbin limamai a Unguwar Kuka a Gundumar Auyo da kuma Chanchandi a Gundumar Mallam Madori.

Sarkin ya kuma hore su da su cigaba da wayar da kan mutane akan halin da ake ciki, musamman lokacin hudabar Juma’a, kuma sai ya gargade su da kada su bari a gansu a inda bai kamata ba.

Sabbin limaman sune Mallam Ibrahim Yunusa da mataimakinsa, Mallam Muhammad Lawan, sai kuma Mallam Shu’aibu Suleiman da mataimakinsa, Mallam Sani Haruna.

A wani labarin kuma, Manajan Yanki na Kamfanin Rarraba Lantarki, KEDCO, Ibrahim Bala Daudu, ya kai ziyarar ban girma ga Mai Martaba Sarkin Hadejia, Alhaji Dr. Adamu Abubakar Maje (CON) a fadarsa dake Hadejia a Jihar Jigawa.

Bayan ya gaishe da Sarki, Manajan sai ya roki sarkin da ya sa a wayarwa da jama’a kai akan muhimmancin biyan kudin wuta akai akai da kauracewa jan wuta ba bisa ka’ida ba, da kuma gujewa biyan kudin wuta ta hannun wadanda ba ma’aikatan KEDCO ba, sannan kuma a gayawa mutane da suyi rijistar wutarsu da kamfanin na KEDCO.

Da yake mayar da jawabi, Sarkin na Hadejia, ya yabawa kokarin  Kamfanin na KEDCO inda yayi kira da su ninka ayyukansu musamman ta hanyar wayawar da jama’a kai akan halin da ake ciki dangane da wutar lantarki.

Sai kuma ya shawarcesu da suyi amfani da kafafen yada labarai wajen ilimintar da mutane hanyoyin da za su bi dan cin gajiyar kamfanin yadda ya kamata.

Leave a Reply

%d bloggers like this: