Gwamna Muhammad Badaru Abubakar ya aike da sakon taya murna ga alummar jihar Jigawa bisa cikarta shekaru 28 da kafuwa
A sakonsa na cikar jihar shekaru 28, Gwamna Badaru Abubakar ya yi kira ga al’umar Jihar na dasu kawar da duk wani banbance banbance su haɗa kai domin ciyar da Jihar gaba.
Gwamna Muhammad Badaru Abubakar yace nasarar da gwamnatin sa ke samu, ya ta’allaƙa ne akan goyon baya da yake samu daga al’umar Jihar nan, tare da zaman lafiyar dake wanzuwa a masarautun jihar nan biyar.
Ya ƙara da cewar gwamnatin sa ta duƙufa wajen farfaɗo da martabar Jihar na, ta hanyar alkinta dukiyoyin al’umma ta hanyar data dace. Daga nan sai Gwamnan ya yabawa tsofaffin Gwamnonin Jihar da sarakuna bisa ƙoƙarinsu na cigaban jihar nan da kuma irin shawarwari da suke bayarwa.