Sakataren Harkokin Wajen Birtaniya Ya Yi Kira Da A Tsagaita Bude Wuta A Kasar Sudan

0 170

Sakataren harkokin wajen Birtaniya James Cleverly ya yi kira da a tsagaita bude wuta tare da kawo karshen tashe tashen hankula a Sudan.

Ya ce an kori jami’an diflomasiyyar Burtaniya daga kasar bayan an yi musu barazana da tashin hankali.

Yanzu haka dai ana cigaba da korar jami’an diflomasiyyar kasashen waje daga Khartoum, a daidai lokacin da sojojin Sudan da wata kungiyar sa-kai ke fafatawa don mamaye babban birnin kasar.

Kashen Faransa, Jamus, Kanada, Spain da Italiya na daga cikin sabbin ƙasashe da suka ba da sanarwar cewa sun kai ma’aikatan diflomasiyyarsu lafiya. Sai dai fararen hula ‘yan kasashen waje suna ta bayar da rahoton cewa ana samun matsala wajen yunkurin ficewa daga Sudan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: