Sakataren Harkokin Wajen Amurka ya sauƙa a Isra’ila don batun zaman lafiya

0 15

Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Antony Blinken, ya sauƙa a Isra’ila don ƙoƙarin farfaɗo da yarjejeniyar dakatar da buɗe wuta a Gaza da kuma tattaunawa kan sako mutanen da aka yi garkuwa da su.

An shirya ziyarar ne, bayan kashe shugaban Hamas, Yahya Sinwar, da Isra’ila ta yi, inda gwamnatin Biden ta ga cewa dama ta samu ta farfaɗo da tattaunawar diflomasiyya.

Sai dai Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ya bayyana ƙarara cewa ba zai daina kai hare-hare ba har sai an murkushe Hamas.

Mai yiwuwa Mista Blinken a yanzu zai mayar da hankali kan yadda za a mulki Gaza bayan rikicin, kuma ƙila zai matsa wa Isra’ila kan barin kayan agaji su shiga arewacin Zirin.

Idan ya bar Isra’ila, Mista Blinken zai kuma nufi ƙasashen Larabawa a ci gaba da tattaunawar.

Ziyarar ta Blinken ita ce ta 11 a Gabas ta Tsakiya tun bayan da aka fara yaƙin Gaza.

  • BBC Hausa

Leave a Reply

%d bloggers like this: