Mutane 6 ake fargabar an kashe tare da kone gidaje da dama a wani sabon fadan kabilanci tsakanin kauyen Bonga a yankin karamar hukumar Konshisha da kauyen Upute a yankin karamar hukumar Oju, dukkansu a jihar Benue ranar Lahadi. Daga cikin gine-ginen da aka kona har da wata coci.
A makon da ya gabata kananan hukumomin biyun suka gwabza fada dangane da wani fili, lamarin da ya jawo mutuwar mutane 2.
An tabbatar da cewa rikicin na ranar Lahadi ya auku kwana daya bayan an gudanar da ganawar neman zaman lafiya a yankin karamar hukumar Konshisha, tsakanin kauyukan biyu da basa ga maciji da juna.
- Gwamnatin Kano ta amince da Naira 71,000 a matsayin mafi ƙanƙantar albashi
- Majalisar Dattawa ta ɗage zaman tantance sababbin ministocin Tinubu
- Gwamnati Tarayya na ɗaukar matakan gyara wutar lantarki – Majalisar dattawa
- Ministan wutar lantarki ya gana da Tinubu kan matsalar wutar arewacin Najeriya
- Kwankwaso yayi Allah wadai da rashin wutar lantarki a Arewa
Wasu ‘yan ta’adda wadanda aka ce suna sanye da kakin soji kuma sun fito daga yankin karamar Konshisha, sun kai hari kan wasu kauyukan.
Wani mazaunin kauyen Upute a yankin karamar hukumar Oju, ya shaidawa manema labarai cewa yan ta’addan sun lalata kasuwanni 2, da shaguna da dama, da sace kaya na miliyoyin naira, yayin da aka raba mata da yara sama da dubu 3 daga gidajensu.