Sabon mafi ƙanƙantar albashi na N70,000 ba shi da wadatar da zai iya biyan buƙatun ma’aikata

Tsohon Shugaban Kasa, Olusegun Obasanjo, ya bayyana sabon mafi ƙanƙantar albashi na naira 70,000 da Shugaba Bola Tinubu ya amince da shi a matsayin maras wadatar da zai iya biyan buƙatun ma’aikata.
A cikin sabon littafinsa mai suna Nigeria: Past and Future, Obasanjo ya zargi shugabannin ƙwadago da fifita muradunsu fiye da walwalar ma’aikata.
Ya ce mafi yawansu suna amfani da mukamansu wajen cimma burin siyasa, lamarin da ke hana su faɗin gaskiya.
Obasanjo ya yi kira da a samar da doka da za ta hana shugabannin ƙwadago shiga siyasa sai bayan sun yi shekara biyar sun bar mukamansu.