Rundunar ‘yansandan jihar Kebbi ta gabatar da cakin kudi na naira miliyan 60 ga iyalan jami’an ‘yansanda 6 da ‘yan fashin daji suka kashe
Rundunar ‘yansandan jihar Kebbi a yau ta gabatar da cakin kudi na naira miliyan 60 ga iyalan jami’an ‘yansanda 6 da ‘yan fashin daji suka kashe a bakin aiki.
‘Yansandan sun rasu yayin arangama da ‘yan fashin daji lokacin da suke aikin gadi a kamfanin kayan abinci na GB a kauyen Gafara dake karamar hukumar Ngaski ta jihar ta Kebbi a ranar 15 ga watan Maris.
Kakakin rundunar ‘yansandan, Nafi’u Abubakar, shine ya sanar da haka cikin wata sanarwa da ya fitar a Birnin Kebbi.
Nafi’u Abubakar yace kwamishinan ‘yansandan jihar, Musa Baba, shine ya mika cakin kudin ga iyalan, a madadin kamfanin na GB.
Kakakin rundunar ‘yansandan ya kuma rawaito kwamishinan na shawarartar iyalan da su yi amfani da kudaden ta hanyar da ta dace wajen farfado da tattalin arzikinsu.