Rundunar ‘yansandan jihar Jigawa ta kama masu laifi guda 17 a wani sumame

Rundunar ‘yansandan jihar Jigawa ta kama masu laifi guda 17 a wani sumame da ‘yansanda suka kai a kananan hukumomin Dutse da Gumel da kuma Ringim.
Kakakin rundunar yansanda ta jiha ASP Lawan Shiisu Adam, shine ya sanar da hakan ga manema labarai a Dutse, inda yace an kai sumamen ne a tsakanin ranakun 17 zuwa 22 ga wannan watan.
Yace an kai sumamen ne domin yaki da masu aikata laifuka a fadin jiharnan.
Shiisu Adam ya kara da cewa a lokacin sumamen, yansanda sun kwace kayayyakin shaye shaye da suka hadar da sholisho da tabar wiwi da kodin da kuma maganin tari na ruwa.
Rahotanni na cewar a ranakun 4 zuwa 10 ga watan da muke ciki, ‘yansanda sun kama masu laifi 10 a kananan hukumomin Taura da kuma Kiyawa na jiharnan.