Rundunar ‘yan sandan Najeriya a jihar Kano ta haramta gudanar da bukukuwan hawan sallah da aka saba yi na al’ada a faɗin jihar

0 177

Rundunar ‘yan sandan Najeriya a jihar Kano ta haramta gudanar da bukukuwan hawan sallah da aka saba yi na al’ada a faɗin jihar.

Cikin wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sandan, Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar, ta ce hakan na cikin shawarwarin tsaro da rundunar ta bai wa mazauna jihar gabanin bukukuwan babbar sallah da za a soma ranar Lahadi.

Sanarwar ta ce rundunar za ta baza jami’anta a sassan jihar domin tabbatar da bin doka da oda a jihar, kafin sallah da lokacin bukukuwan bayan sallar. Sanarwar tace haka kuma an haramta duka nau’ikan hawan sallah a lokacin bukukuwan babbar sallah da ke tafe

Leave a Reply

%d bloggers like this: