Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa ta tarbi sabbin ‘yan sanda 448 da suka kammala horon su na tsawon wata shida a Kwalejin ‘Yan Sanda ta Kaduna.
Kwamishinan ‘yan sanda na jihar, Ahmad Abdullahi, ya yi gargadi ga sabbin jami’an da su zama masu da’a, su kiyaye dokokin aiki tare da mutunta ‘yancin jama’a.
Ya kuma ja hankalinsu da su kaucewa karbar rashawa da daukar bashi da zai iya jefa su cikin matsala.
Sabbin jami’an za su kara samun horo a fannonin amfani da makamai, dabarun yaki da kuma aiki a filin daga domin tabbatar da cikakken shiri na aikin su.