Rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa ta gurfanar da wasu mutane 58 a gaban kotu

0 246

Rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa ta gurfanar da wasu mutane 58 da ake zargi da aikata laifuka da kuma kwato makamai a hannunsu.

A yayin da yake gabatar da wadanda ake zargin CP Dankombo Morris, ya bayyana cewa dukkan wadanda ake zargin sun amsa laifukan da suka aikata kuma za su fuskanci hukunci a gaban kotu.

Ya jaddada kudirin rundunar na rage aikata laifuka, inda ya kara da cewa ’yan kungiyar asiri su ne babban kalubale ga matsalar tsaro a jihar.

Ya ce rundunar ‘yan sanda ta kaddamar da wani shiri na hadin gwiwa tare da mafarauta a ranar 16 ga Maris, a dajin Sambisa dake jihar Adamawa, inda suka kama ‘yan kungiyar asiri 40 tare da kwato makamai. CP Morris ya kuma kara da cewa ‘yan sanda sun kama wasu gungun ‘yan fashi da makami guda biyar a cikin Jimeta, wadanda suka yi wa fasinja da mutanen da ke cikin motocinsu fashi daga jihar Taraba suka tsere zuwa jihar Adamawa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: