Rundunar ‘yan sanda a Jihar Yobe ta kuɓutar da wani ƙaramin yaro daga hannun masu garkuwa da mutane

0 143

Rundunar ‘yan sanda a Jihar Yobe ta kuɓutar da wani ƙaramin yaro mai suna Adamu Sani daga hannun masu garkuwa da mutane.

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan, DSP Dungus Abdulkareem ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a Damaturu, babban birnin Jihar Yobe.

Ya ce jami’an ‘yan sanda hedikwatar da ke Gujba ne suka kuɓutar da yaron tare da kama jagoran masu garkuwar.

Bayanai sun ce, lamarin ya faru ne a lokacin da wasu ‘yan bindiga suka kutsa cikin ƙauyen Bungai na garin Buni Yadi da ke Ƙaramar Hukumar Gujba.

DSP Dungus ya ce maharan sun riƙa harbi da baka da kibiya da kuma bindiga, lamarin da ya basu damar yi wa mazauna yankin barazana tare da awon gaba da yaron mai shekara uku.

Leave a Reply

%d bloggers like this: