Rundunar Sojoji ta ce ta kama wasu ƙasurguman ‘yan bindiga biyu a jihar Taraba

0 162

Wata sanarwa da mataimakin kakakin runudunar, Kanal Oni Olubodunde, ya fitar ta ce dakarun rundunar Operation Whirl Stroke ne suka yi nasarar kama mutanen da ba ta bayyana sunansu ba a ranar Alhamis.

A cewar sanarwar samamen da dakaru suka kai bayan tattara bayanan sirri a ƙauyen Geshi na ƙaramar hukumar Donga a jihar Taraba ya yi sanadiyyar ƙwato babur biyu da ‘yanta’addan ke amfani da su.

Ta ƙara da cewa an samu bayanan sirrin ne bayan wasu mahara sun kai hari, inda dakaru suka ɗunguma zuwa Geshi kuma suka fara musayar wuta da su abin da ya sa suka tsere zuwa cikin daji.

Leave a Reply

%d bloggers like this: