Rundunar sojin sama ta yi nasarar hallaka ‘yan ta’adda da masu garkuwa da mutane akalla 30

0 320

Rundunar sojin saman kasa ta yi nasarar hallaka ‘yan ta’adda da masu garkuwa da mutane akalla 30 a wani harin da ta kai ta sama a yankin Kwiga-Kampanin Doka a karamar hukumar Birnin Gwari ta jihar Kaduna.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Daraktan hulda da jama’a da yada labarai na rundunar sojojin saman kasa, AVM Edward Gabkwet, ya fitar a jiya Litinin a Abuja.

Gabkwet ya ce sumamen ya biyo bayan bayanan sirri ne da aka samu kan zirga-zirgar masu aikata laifuka a yankin.

Ya kuma kara da cewa, rundunar ta kuma bayyana cewa kungiyar ce ke da alhakin yi wa sojoji kwanton bauna a ranar 27 ga watan Janairu, da kuma wasu hare-hare da sace-sacen jama’a da ba su ji ba ba su gani ba a Birnin Gwari.

A cewarsa, cikakken bincike ya gano yadda ‘yan ta’adda ke tafiya a cikin ayarin motoci kusan 15, kowannensu dauke da akalla ‘yan ta’adda biyu dauke da makamai. Gabkwet ya ce nasarar harin da aka kai ta sama ya jawo hankalin babban hafsan hafsan sojin sama Air Marshal Hasan Abubakar, inda ya yabawa kwamandan da rundunarsa bisa yadda suka yi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: